27 Yuli 2020 - 11:20
An Yi Arangama Tsakanin ‘Yan Sanda Da Masu Bore A Amurka

Rahotannin daga Amurka na cewa an yi arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga a biranen kasar da dama.

ABNA24: Bayanai sun ce an yi zanga zangar a biranen da suka hada da Austin, Louisville, New-York da Los Angeles kan nuna wariyar launin fata da kuma shirin shugaban kasar Donald Trunp, na jibge dakarun tarayya a birane.

Saidai a wasu biranen gangamin ya rikide zuwa tarzoma inda ‘yan sanda sukayi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga zangar.

342/